Ina kira ga mutanen Borno su kyale Zulum ya ci gaba da mulki har illa masha Allahu—El-rufai

Gwamnan jihar Kaduna Mlm. Naseer El-rufai ya shawarci mutanen jihar Borno da su bar gwamnan Zulum ya ci gaba da mulki har illa masha Allahu, kamar yadda shafin Labarun Hausa ya ruwaito.

Bayan kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar Borno tayi, gwamnan Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi kira ga mutanen jihar Borno akan kara zaben Babagana Zulum a karo na biyu, Leadership ta ruwaito.

Ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a Maiduguri yayin da ya halarci taron kaddamar da wasu ayyukan gwamnatin jihar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

Views: 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *