
Allah Madaukakin Sarki ya kafa hujja wa Kiristoci a kan bacin Addininsu da a ce suna da lura da fahimta. Allah yana magana a kan Annabi Isa (as) sai ya ce:
{وَأُمُّهُ صِدِّيقَةٌ كَانَا يَأْكُلَانِ الطَّعَامَ} [المائدة: 75]
((Mahaifiyarsa Mai yawan gaskiya ce, kuma sun kasance su biyun (Shi da Mahaifiyarsa) suna cin abinci)).
Wannar Ayar ta kunshi manyan dalilai guda uku da suke rushe Akidar cewa; Annabi Isa (as) Allah ne.
1- Dalili na farko: Kasancewar haifuwarsa aka yi:
Lallai duk wanda aka haife shi, to ba zai taba zama Allah abin bauta ba. Don haka kasancewar Annabi Isa (as) yana da Uwa wannan ya nuna cewa; haifuwarsa aka yi. Allah kuwa ba a haifarsa. Al-Qurdubiy ya ce:
(({وأمه صديقة} ابتداء وخبر {كانا يأكلان الطعام} أي أنه مولود مربوب، ومن ولدته النساء)).
تفسير القرطبي (6/ 250)
((Mahaifiyarsa Mai yawan gaskiya ce, ma’ana; lallai haifuwarsa aka yi, halittarsa aka yi, kuma wanda mace ta haife shi)).
2- Dalili na biyu: Kasancewarsa yana cin Abinci:
Kasancewar Annabi Isa (as) yana cin abinci ya nuna yana da bukata, Allah kuwa Mawadaci ne, ba ya bukatar komai a wajen kowa, shi ya sa ba ya ci, ba ya sha. Wannan ya sa al-Sam’aniy ya ce:
(({كانا يأكلان الطعام} أي: يتغذيان بالطعام، ومعناه: أن من يتغذى بالطعام لا يكون إلها يعبد)).
تفسير السمعاني (2/ 56)
((Ai suna cin abinci. Ma’anar haka: lallai duk wanda yake cin abinci ba zai kasance Allah abin bauta ba)).
Don haka kasancewar Annabi Isa (as) yana cin abinci, hakan yana lazimta dole ya zama yana da ciki, da wurin fitan abincin, wannan ma wani dalili ne da yake tabbatar da cewa; Annabi Isa (as) ba Allah ba ne, saboda duk wanda yake haka bai cancanci ya zama Allah abin bauta ba. Saboda Allah “al-Samadu” ne, ba shi da ciki da hanji. Ibnu Taimiyya ya ce:
((قال: {كانا يأكلان الطعام} وهذا من أظهر الصفات النافية للإلهية لحاجة الأكل إلى ما يدخل في جوفه ولما يخرج منه مع ذلك من الفضلات. والرب تعالى أحد صمد لم يلد ولم يولد ولم يكن له كفوا أحد)).
الجواب الصحيح لمن بدل دين المسيح لابن تيمية (2/ 171)
((Fadinsa: {Sun kasance su biyun (Shi da Mahaifiyarsa) suna cin abinci}, wannan yana daga cikin mafi bayyanar Siffofi masu kore Allantaka, saboda bukatar ci ga abinci da zai shiga cikinsa, da kuma bukatuwa zuwa ga abin da zai fita daga gare shi na bayan gari. Allah Ubangiji Madaukaki kuwa shi kadai ne, kuma ba shi da ciki, bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani da yake daidai da shi)).
3- Dalili na uku: Kasancewar yana yin bayan gari:
Kuma kasancewar Annabi Isa (as) yana cin abinci ya nuna cewa; lallai dole ya yi bayan gari, saboda yinsa lazimin cin abinci ne, wato shi ne fitar da abincin a bayan gida. Kamar yadda Ibnu Qutaibah ya ce:
((وقوله: {كانا يأكلان الطعام} هذا من الاختصار والكناية، وإنما نبه بأكل الطعام على عاقبته وعلى ما يصير إليه وهو الحدث؛ لأن من أكل الطعام فلا بد له من أن يحدث)).
غريب القرآن لابن قتيبة ت أحمد صقر (ص: 145)
((Wannar Ayar ta gajarta bayani kuma ta yi kinaya (saye), Allah ya fadakar da maganar cin abinci a kan abin da zai biyo bayansa, da abin da abincin yake zama, wato bayan gari. Saboda duk wanda ya ci abinci to dole sai ya je ya yi bayan gari)).
Ibnu Taimiyya bayan ya ambaci fassarar Ibnu Qutaiba sai ya ce:
((وهذا الوجه صحيح في حق المسيح وأمثاله من البشر في الدنيا، فإن أكلهم الطعام يستلزم الحدث، وخروج الحدث من أبين الأشياء دلالة على انتفائه إلهية من يبول ويغوط، وذلك أعظم من كونه يلد)).
جامع المسائل لابن تيمية ط عالم الفوائد (1/ 116)
((Wannar fiska ingantacciya ce a game da Almasihu da makamantansa cikin mutane a Duniya, saboda cin abinci yana lazimta yin bayan gari. Kuma fitan bayan gari yana daga cikin abubuwa bayyanannu da suke nuni a kan kore Allantakar wanda yake fitsari da bayan gari, wannan kuma ya fi ma girma a kan kasancewarsa yana haifuwa)).
Saboda haka a cikin wannar gajeruwar Ayar, Allah ya kunsa dalilai har guda uku da suke nuna bacin Addinin Kiristoci.
✍️Aliyu Muh’d Sani
Views: 19
