Ina roƙon Allah ya fito wa da ƴata mijin aure na gari—Hadiza Saima

A ƙarshen makon daya gabata ne kafafen sada zumunta na zamani wato Social Media suka cika da hotunan ƴar gidan shahararriyar jarumar fina finan Hausa ta Kannywood Hadiza Saima.

Inda aka ambato ta tana cewar ita a halin yanzu babu abinda take son gani kamar ranar auren ƴarta guda ɗaya tilo da take da ita, jaruma Hadiza Saima tace tana fatan Allah SWT ya fito wa da wannan ɗiya tata mijin aure na gari.

Wasu dai na sukar jaruman masana’antar Kannywood inda suke cewar menene dalilin da yasa basa sanya ƴaƴan su a cikin shirin film? Idan har dagaske tarbiyya suke koyarwa ya kamata su riƙa saka ƴaƴan su a cikin sana’ar.

A wani labarin kuma

Duka dai a Cikin Shagulgular gudanar da bukukuwan ibada na Kirsimeti a Habasha.

Kirsimeti a Habasha ana kiransa da suna “Ganna ko Genna” kuma ana yin bikin ne a ranar Bakwai ga watan Janairu.

Kamar yawancin majami’un Orthodox na duniya, bikin Kirsimeti ya na gudana ne a ranar 7 ga Janairu a Habasha.

Kamar dai yadda watannin kalandar Habasha suka bambanta, bikin Ganna ya kasance ne a ranar 29 ga watan Tahsas.

Cocin Orthodox na Habasha ta ɗauki 7 ga Janairu a matsayin ranar haihuwar Yesu don haka ita ce ranar manyan ayyukan addini a Habasha.

Ƙarin bayani: Shekarar da muke ciki a Habasha ita ce shekarar 2015. Shekarar Habasha ta na farawa ne a ranar 11 ga Satumba ko kuma a ranar 12 ga Satumba a shekara ta miladiyya.

Daga Taskar Nasaba.

Views: 30

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *