Inna lillahi Wa’inna Ilaihin Raji’un Allah mun tuba ku kalli yadda ake tarwatsa garuruwan arewa

Wani rahoto da sashin Hausa na BBC ya bayar ya ambato Garba Shehu na cewa, mun gama dukkanin shirye-shiryen kawo karshen hare-haren ta’addanci a Arewacin Najeriya na har abada.

Mai bai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shawara kan yada labarai Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa za a hada hannu da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen kasar domin kawo karshen matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na har abada.

A yau Lahadi ne aka soma taron shugabanin kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO karo na 60 a Abuja.

Wannan taro zai gudana ne a daidai lokacin da yawancin kasashen na yammacin Afrika ke cikin wani yanayi na tsananin rashin tsaro, lura da yadda kungiyoyin tayar da kayar baya da sauran ‘yan bindiga suka addabe su.

A ‘yan kwanakin nan mahara sun kona matafiya sama da 42 a jihar Sokoto, kuma kafin nan wasu maharan sun kona wasu matafiyan da ke hanyar su ta zuwa kasuwa a Mali.

Garba Shehu ya ce, ” Shugaban kasa ya tura wakilci na musamman na masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaron kasa musamman samar da bayanan sirri, kuma sun je sun tattauna da wakilai a matakin kananan hukumomi da jihohi sun dawo masa da rahoto, kuma za a ga abin da zai biyo baya.”

Kazalika ya ce a matakin kasa da kasa, taron na ECOWAS ko kuma CEDEAO zai ba da tasa gudummuwa wurin kawo karshen hare-hare a Arewacin Najeriyar.

” Wannan batu yana daya daga cikin ajanda da Shugabanni za su tattauna. Abu ne da ya damu kowa, ba a jin dadi, kuma babu wani Shugaban kasa da za a ce hankalinsa ya kwanta da wannan fitina da ake fama da ita. Saboda haka za a dauki mataki nan ba da jimawa ba za a kawo karshen hare-hare a arewacin Najeriya na din-din-din,” a cewar Garba Shehu.

Views: 26

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *