Jami’an ƴan sanda sun kama Matar da ta Lakaɗawa mahaifiyar ta duka a jihar Anambra

Jami’an ƴan sanda sun kama Matar da ta Lakaɗawa mahaifiyar ta a jihar Anambra

Jami’an ƴan sanda sun yi caraf da matar da ta lakaɗawa dattijuwar mahaifiyarta dukan tsiya a jihar Anambra.

An cafke matar ne bayan bayyanar bidiyonta tana cin zarafin dattijuwar mahaifiyarta lokacin da ta ke mata wanka.

An yi Allah wadai da halin rashin darajar da matar ta nuna ga dattijuwar mahaifiyarta mai shekara 75 a duniya

Jihar Anambra – Ƴan sanda a jihar Anambra sun cafke wata mata mai suna Ukamaka Udugbo mai shekara 50 a duniya bisa lakaɗawa mahaifiyarta mai shekara 75 duka a yankin Abagana na ƙaramar hukumar Njikoka ta jihar.

Matar dai an ɗauke ta ne a cikin wani faifan bidiyo tana cin zarafin mahaifiyarta ta hanyar lakaɗa mata duka, cewar rahoton PM News.

‘Yan sanda sun cafke matar da ta yi wa mahaifiyarta
Dattijuwar da aka lallasa da duka Hoto: Pmnews.com Asali: UGC.

DPO na ofishin ƴan sandan Abagana, SP Ifeanyi Umeh shi ne ya tabbatar da cafke matar da lokacin da wata ƙungiya mai zaman kanta ’50-50 Action Group of the WomenAid Collective’ (WACOL) ta ziyarce shi kan lamarin.

Umeh ya bayyana cewa sun samu labarin yadda matar ta ci zarafin mahaifiyarta mai suna Theresa Nwaokaka, wanda hakan ya sanya suka yi gaggawar zuwa cafko ta.

Views: 27

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *