
Jihar Kano Za Ta Goyi Bayan Burin Tinubu Na Zama Shugaban Ƙasa, Inji Gwamnatin Jihar Kano
Jihar Kano za ta goyi bayan burin jagoran jam’iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023, kamar yadda Kakakin majalisar dokokin jihar, Hamisu Chidari ya bayyana.
Chidari yabayyana haka ne a lokacin ƙaddamar da ƙungiyar tallafawa Tinubu da kwamitocin gudanarwa na TSG a Abuja ranar Asabar.
Ya ce jihar Kano, wacce ke da mafi yawan masu jefa ƙuri’a da wakilai a cikin ƙasar, za ta rama aikin Tinubu na taimaka wa Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya zama Shugaban ƙasa a 2015.
“Manufata ita ce fara tafiya wanda zai kai mu Villa da yardar Allah tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan Najeriya na ɗaya.” In ji shi
Shugaban majalisar ya ƙara da cewar, “A Kano kasancewar jihar da ke da mafi yawan wakilai, mun riga mun yanke shawara kuma mun kammala; muna shirin ba shi aƙalla kashi 98 na wakilai a zaɓen fidda gwani. Ba wannan kaɗai ba, an shirya kamar yadda muka saba don ba shi mafi yawan ƙuri’un don haka a ranar 29 ga Mayu, 2023, za mu kasance a Dandalin Eagle Square don rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.”
“Dukkan mu a Arewa maso Yamma muna sane da rawar da ya taka wajen kai ɗan mu, shugaba Muhammadu Buhari, zuwa Villa. Don haka, za mu ba shi lada; za mu biya shi. Don haka, na ba shi tabbacin nasara. Kusan dukkan wakilai daga jihohin Arewa maso Yamma za su zaɓe shi a zaben fidda gwani na gaba.” Inji Chidari.
©Idon Mikiya
Views: 8
