Kai Ne Za Ka Gyara Kanka Da Kanka

Kai Ne Za Ka Gyara Kanka Da Kanka.

©️ Abdulhadi Aminu.

Fitowa daga gidan kirki ba shi ke nuna kai na kirki ne ba, wannan sanannen abu ne a addinin Musulunci.

Abu Ɗalib a.s mahaifin Imam Ali a.s ya kasance cikakken mumini mai kariya ga Annabi s.a.w.w, wanda har Annabi s.a.w.w ya sanya wa shekarar da ya rasu “Shekarar Baƙin Ciki”. A lokaci guda kuma Abu Lahab ya kasance mafi tsananta adawa da ƙiyayya ga Annabi s.a.w.w, ya kasance mara rabo a matakin farko.

Abin mamaki shi ne dukansu a gida ɗaya suka tashi, mahaifi ɗaya, tarbiyya ɗaya, kuma yanayin rayuwa ɗaya, ka ga ashe abin ba wai daga iya tarbiyyar da ake baka a gida ba ne, domin da haka ne da Abu Lahab bai zamo abin da ya zamo ba.

Duk irin tarbiyyar da ake baka a gida idan baka shirya zama na kirki ba hakan ba zai amfane ka da komai ba, dan haka komai a hannunka yake, kuma za ka iya zama yadda kake so inma na kirki ko na banza.

Allah ka sa mu kasance cikin mutanen kirki da za ka yi amfani da su domin taimakon addini da al’umma.

Views: 25

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *