
A makon daya gabata ne wasu daga cikin manyan jami’o’in tarayyar Najeriya suka haramtawa dalibai gudanar da al’adar nan ta sign out ga daliban su sakamakon yin abubuwan da basu dace da koyar war addini da al’adu ba, makarantar farko da ta fara soke wannan bakar al’ada dai ita ce jami’ar Umaru Musa Yar’adua University Of Katsina (UMYUK).

Sai kuma daga baya bayannan inda wata jami’a a jihar Kebbi ita ma tabi sahun UMYUK din wajen sokewa ko kuma haramta al’adar ta sign out ga daliban jami’ar ga kadan daga cikin wasu hotunan sign out da daliban ke yi a duk lokacin da suka kammala zana jarabawar su ta karshe wato final examination.
Tuni wasu daliban ke Allah wadai da wannan haramci wanda makarantun nasu ke yi, yayin da wasu ke nuna goyon bayansu kan hukuncin, wanda ake sa ran sauran jami’o’in da ke fadin kasar ta Najerya za su bi sahun takwarorinsu wajen soke wannan bakar al’ada.
Views: 75
