Ku kalli shirin labarina kashi na 2 zango na ukku kai tsaye yanzu

Shahararren shirin nan mai farin jini wato Labarina wanda kamfanin shirya fina finai na Saira Movies ke gabatarwa a tashar Arewa24 ya sake fitowa yau a ranar Juma’a kuma yanzu haka za ku iya kallon shirin a shafin Saira Movies da ke a dandalin sada zumunta na YouTube.

Dama dai tun a farkon watan da ya gavata ne dai mai shirya shirin na Labarina Malam Aminu Saira ya sanar da yau Jumu’a biyu ga watan bakwai a matsayin ranar da za’a ci gaba da haska shirun zango na ukku wanda kuma tuni an haska shi a makon daya gabata yau ma ana haska shirin a Saira Movies YouTube.

Wannan shirin na Labari dai shiri ne wanda ya yi fice musamman ga masu jin harshen Hausa a fadin Najeriya da ma kasashen duniya, a halin yanzu dai shirin ya fito ga duk mai bukatar kallonsa sai ya garzaya zuwa shafin YouTube ya nemi tashar Saira Movies don kallon shirin film din na Labarina.

Views: 55

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *