
Shahararren shirin nan mai farin jini wato Labarina wanda kamfanin shirya fina finai na Saira Movies ke gabatarwa a tashar Arewa24 ya sake fitowa yau a ranar Juma’a kuma yanzu haka za ku iya kallon shirin a shafin Saira Movies da ke a dandalin sada zumunta na YouTube.
Dama dai tun a farkon watan da ya gavata ne dai mai shirya shirin na Labarina Malam Aminu Saira ya sanar da yau Jumu’a biyu ga watan bakwai a matsayin ranar da za’a ci gaba da haska shirun zango na ukku.
Shirin Labari dai shiri ne wanda ya yi fice musamman ga masu jin harshen Hausa a fadin Najeriya da ma kasashen duniya, a halin yanzu dai shirin ya fito ga duk mai bukatar kallonsa sai ya garzaya zuwa shafin YouTube ya nemi tashar Saira Movies don kallon shirin.
Views: 51
