LABARI DA DUMI DUMI: “Abdul’aziz Yari zai fice daga APC

Hoton Yari da Marafa

Wani magoyin bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, mai suna Mustapha Isa Gusau, ya ce a shirye suke da su balle daga jam’iyyar APC domin nemawa kansu mafita a siyasance matukatar jagoransu ya nemi da suyi hakan saboda ba za su yarda ace gwamna Matawalle ya kankame komai a jam’iyyar ba.

A wani labarin na daban kuma.

An Bukaci Jam’iyar APC ta kasa da ta ladabtar da Yari da Sanata Kabiru Marafa.

Wani daya daga cikin fitattun ‘yansiyasar jihar Zamfara kuma tsohon dankaran gwamna a jam’iyar APGA, kuma mamba a jam’iyar APC, Alh Abdullahi wamban Shinkafi, ya yi kira ga uwar Jam’iyar su ta APC data hukunta Abdul’aziz Yari da Kabiru Marafa saboda karya dokar da ke cikin kundin tsarin mulkin jam’iyar ta APC.

Mr, Shinkafi ya yi wannan kiran ne ga manema labarai a Gusau , babban birnin jihar, ya ce hakan ya biyo bayan taron da su Abdul’aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa da wasu ‘yayan jam’iyar suka yi a Kaduna , bayan ficewar gwamna Bello Mohammed Matawalle da magoya bayansa daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyar APC a hukumance a ranar Talatar da ya gabata.

Jigon mai suna Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi ya bukaci a kaka bawa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdul’Aziz Yari Abubakar takunkumi mai tsauri saboda sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, ya ce dole ne a dauki tsauraran matakai a kan Yari da kabiru Marafa na jam’iyyar ta APC .

Kamar yadda ya bayyana a wajen taron da Yari da Kabiru da magoya bayansu suka yi a Kaduna inda suka yi tir da umarnin shugabannin jam’iyyar na kasa kan rusa shugabannin jam’iyyar a dukkan matakai a jihar da cewa cin fuska ne ga Shugaba Muhammadu Buhari da dukkanin shugabannin jam’iyyar na kasa, gaba daya.

Views: 54

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *