Kyakkyawar Baturiya ta kai saurayinta ɗan Najeriya gaida surukai

Kyakkyawar Baturiya ta kai saurayinta ɗan Najeriya gaida surukai

Wata zankaɗeɗiyar baturiya wacce bata san yadda iyayenta za su tarbi saurayin ta ɗan Najeriya ba, tayi ta maza ta kai shi gida.

Suna isa gidan mahaifan nata, sai iyayen ta suka tarbe shi hannu bibbiyu domin nuna cewa sun yi na’am

Ƴan Najeriya da dama waɗanda suka yi tsokaci a kan bidiyon masoyan biyu sun fatan samun irin wannan soyayyar ta su.

Wata kyakkyawar baturiya ta sanya wani bidiyo wanda ya nuna lokacin da ta kai saurayin ta ɗan Najeriya gida domin ya haɗu da iyayen ta.

Budurwar tace tayi zullumin cewa iyayen ta ba zasu yi maraba da shi ba. Sai dai hakan ba shine abinda ya faru ba domin sun tarbe shi hannu bibbiyu.

A cikin bidiyon an nuna yadda matashin ɗan Najeriya da mahaifiyar budurwar tasa suka buga kwallon kwando tare. Mahaifinta shima ya sakar masa fuska inda suka yi ta ayyuka tare.

Mutane da dama waɗanda suka yi tsokaci akan bidiyon, sun yi magana kan yadda soyayyar su ta zama abin ban sha’awa.

Source:hausa legit.ng

Views: 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *