Labarin wasu masoya ɗan India da Ƴar Pakistan da soyayyar su ta ƙare a gidan yari

Labarin wasu masoya ɗan India da Ƴar Pakistan da suka ƙare a gidan yari

A watan Janairu, an kama wani Ba’indiye da ya taimaka wa wata ‘yar Pakistan da ta shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba ta kuma samu katin shaida na bogi.

Matar da ya taimaka matarsa ce.

Mulayam Singh Yadav, ɗan shekara 21 ɗan asalin India da Iqra Jeewani mai shekara 19 wadda ta fito daga Pakistan sun haɗu ne a intanet shekara uku baya, daga nan suka fara soyayya, kuma sun fara ne ta hanyar yin wsan Ludo. Amma sun san abu ne mai wuya su kasance tare.

Alaƙa tsakanin India da Pakistan ta jima a matsayin marar daɗi – makotan sun yi yaƙi tsakaninsu sau uku tun daga shekarar 1947, lokacin da India ke fafutukar neman ‘yanci ita kuwa Pakistan ta ƙirƙiri nata.

Wannan ya sanya samun biza tsakanin ƙasashen biyu masu tarihi ɗaya yake da wuya.

A watan Satumbar da ya gabata ne, Mulayam da Iqra suka je Nepal, suka yi aure a can. Daga nan kuma suka tafi Bangalore babban birnin Karnataka inda suka ci gaba da rayuwa.

Rayuwar da suke yi mai daɗi ta koma ta wuya a watan Janairu- An tsare Iqra saboda ta shiga India ba ta hanyar da ta dace ba, shi kuwa aka kama shi saboda aikata laifin zamba cikin aminci da yi wa wani takardun ƙarya da kuma bai wa ɗan ƙasar waje wurin zama ba tare da cikakkun takardu ba.

An mayar da ita Pakistan a makon jiya, shi kuwa an ci gaba da tsare shi a gidan yari da ke Bangalore.

‘Yan uwan Yadav, wanda ke zaune a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin India, sun ɗimauta da kamun da aka yi masa.

“Muna fatan muga sun dawo gida,”. “Mun san abin da ke tsakanin India da Pakistan. Amma su masoya ne kawai,” in ji Jeetlal dan uwan Yadav.

Ko ‘yan sanda sun yi kamar sun yarda.

“Bayan shiga ba bisa ƙa’ida ba da takardun bogi, sai kuma labarin soyayyarsu,” in ji wani babban jami’in ‘yan sanda da ya nemi a boye sunansa.

Masoyan sun yi aure a bara, sai dai ba su ɗauki lokaci suna rayuwa ba tare.

Source:BBC.com

Views: 25

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *