
Labarai: a jiya ne ɗan takarar neman kujerar shugabancin Najeriya Alhaji Bola Ahmad Tunubu ya yi jawabi a birnin London.
A CHATHAM HOUSE….
An yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tambayoyi ne guda Goma, a tsarin shugabanci da salon Tinubu, sai ya zabi ya amsa Hudu sannan ya bawa mutanensa damar amsa sauran tambayoyi guda shida, Mutanen nasa sune…
Governor El-Rufai
Femi Gbajabiamila
Betta Edu
Wale Edun
Dele Alake
Ben Ayade
Hakan ba sabon abu bane a wajen Bola Tinubu a lokacin da yake Gwamnan Lagos irin wannan tsarin yake bi a lokacin da zai gana da yan jaridu, yakan bawa kowanne Kwamishina damar amsa tambayar data shafi ayyukansa, irin dai yadda shugabannin Amurka keyi…
Idan Bola Ahmed Tinubu ya zama Shugaban Nigeria zai cigaba da irin wannan tsarin na bayar da damar ga Ministoci su dinga amsa tambaya kai tsaye a duk lokacin da zai gabatar da taron manema labarai, Tinubu ya yadda da za’ban mutanen da suka cancanta a kowanne bangare tare da basu damar nuna bajintarsu, kamar dai yadda a yau ma ya bawa mutanensa damar amsa tambayoyi..
Wanna ziyara da ɗan takarar na shugaban kasar Najeriya a ƙarƙashin tutar jam’iyyar All Progressive Congress wato APC a taƙaice Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tunubu ya kai ta al’ada ce ganin cewa dama Shugabanni da manyan.
ƴan siyasar Afrika suna kai makamanciyarta.
Asiwaju zai samar da Jajirtattun Ministoci, da sauran ma’aikatan Gwamnati, idan ya zama shugaban Nigeria….
Hakan ba sabon abu bane a wajen Bola Tinubu a lokacin da yake Gwamnan Lagos irin wannan tsarin yake bi a lokacin da zai gana da yan jaridu, yakan bawa kowanne Kwamishina damar amsa tambayar data shafi ayyukansa, irin dai yadda shugabannin Amurka key.
Kamar yadda masuya bayansa ke ƙara nanatawa idan Bola Ahmed Tinubu ya zama Shugaban Nigeria zai cigaba da irin wannan tsarin na bayar da damar ga Ministoci su dinga amsa tambaya kai tsaye a duk lokacin da zai gabatar da taron manema labarai, Tinubu ya yadda da za’ban mutanen da suka cancanta a kowanne bangare tare da basu damar nuna bajintarsu, kamar dai yadda a yau ma ya bawa mutanensa damar amsa tambayoyi..
Views: 22
