LABARAI DA DUMI DUMI: “Dagaske ana zanga zangar kama Abduljabbar?”

A safiyar ranar Asabar ne wasu daga cikin shafukan sada zumunta suka rika yada labarai cewa, ‘Almajiran Sheakh Malam Abduljabbar sun kira zanga zangar gama gari domin kira ga hukumomi da su saki malamin’ sai dai Magoya bayan malamin sun karyata wanna batu ga rubutun da suka yi a kai inda suka ce.

DUK WANDA KUKAJI YACE KUYI ZANGA-ZANGA KU QARYATA SHI.

Asiri Ya Tonu, Sabon Makircin ‘Yan Maja Maqiya Allah Da Manzon Allah saww.

Yanzu Muke Sami Labari Wadannan Fasiqan (‘Yan Maja) Suna Yada Qarya Da Sharri Cewa: Wai ‘Yan As’habul kahfi Suna Gayyatar Zanga-Zanga, TO QARYA NE.

Muna Kira Ga Hukuma Da Yawun Maulana Dr Sheikh Abduljabbar (H), Mun Barranta kanmu Akan wannan Sanarwa Da Take Yawo A Social Media, Domin Qarya Akeyiwa ‘Yan As’habul kahfi, Babu Hannu Su Babu Hannun Jagiran Su Amirul Wa’izeena Kabara (H).

Don Haka Duk Wanda Aka Gani, Ya Fito Zanga-Zanga, Wallahi Ba Dan As’habul kahfi Bane, Kuma Maqiyin As’habul kahfi Ne, Maqiyin Sheikh Abduljabbar (H), Kawai Malaman Su Na Maja Ne Suka Umarce Su Don Su Kunna Wata Sabuwar Fitinar A Rigar As’habul kahfi, A Qarshe Akarkashe ‘Yan As’habul kahfi Zulman, Tunda Anga Duk Abinda Za’ayi Na Makirci Don Su Tunzura Allah Yaqi Amincewa.

Kuma Har Abada Mu Bazamuyi Zanga-Zanga Ba, Domin Zanga-Zanga Babu Maiyinta Sai Mai qarancin Imani: Ma’ana:- Wanda Bai Miqa Lamuransa Zuwa Ga Allah Ba, Mu Kuma Taken Ken Mu Shine حسبنا الله ونعم الوكيل.

A Qarshe, Kira Ga ‘Yan As’habul kahfi, Mu Tsaya Tsai Mu Mallaki Hankalin Mu, Mu Sanya Hikma, Juriya Da Haquri, Tareda Tsayuwa kan Gaskiya Duk Rintsi Ba Tare Da Juya Mata Baya Ba, Sannan A Yada Wannan Saqon Ta Ko’ina Har Allah Ya Bamu Galaba Akan AKan Azzalumai Maqiya Manzon Allah saww.

Irin Su Malam Abduljabbar Kabara, Su Allah Yake Yiwa Tambari Da
“مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَيْهِ ۖ فَمِنْهُم مَّن قَضَىٰ نَحْبَهُۥ وَمِنْهُم مَّن يَنتَظِرُ ۖ وَمَا بَدَّلُواْ تَبْدِيلًا”
~Mujamma’u As’habul Kahfi Warraqeem.
Assabar 17th July 2021.

Sunyi wannan rubutu ne a shafinsu na Facebook kamar yadda za kuga hoton rubutun daga kasa

Daya daga cikin shafukan da suka yada labarin zanga zangar dai shine Hausa Daily inda suka ce

YANZU-YANZU: An Fara Zanga Zanga Akan Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara A Kano

An fara kiraye-kirayen A saki Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Me zaku ce?

Ga hoton rubutun

Views: 34

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *