Dalilin da ya sa yan sanda suka kama Abduljabbar

A ranar juma’ar da ta gabata ne jami’an tsaron yan sanda suka kama fitaccen malamin addinin islamar nan da ya jawo ce-ce-ku-ce Sheakh Abduljabbar Sheakh Nasiru Kabbara wanda kawo suka gurfanar da shi gaban Kotu yayin da alkalin Kotun ya bada umarnin tasa keyarsa zuwa gidan maza.

Kawo yanzu dai hukunar yan sanda tana tsare da malamin gabanin ta kai shi gidan yarin sai dai har yanzu hukunar bata bayyana dalilan da suka sanya ta kama malamin amma dai ta gayyace shi a makon da ya gabada inda ake hasashenta ja masa kunne ne game da bin doka da oda.

Amma ana zargin kamu nasa yana da alaka da wasu shirye shiryen bidiyo da ya rika yadawa kai tsaye ta kafar sadarwar Facebook, inda yake kalubalantar sahihancin mubalar da aka gudanar tsakaninsa da malaman jihar duk kuwa da cewa kowa yaga irin adalcin da aka yi masa wajen shirya mukabalar.

Views: 2

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *