’Yan uwa, ina so in yi amfani da wannan dama domin in sake gode muku da kuka zabe ni in zama shugaban ku a lokuta biyu.
Ni ba dan takara ba ne a wannan zaben, amma jam’iyyata ta APC tana da dan takara a matsayin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Kamar yadda na ambata a baya, Tinubu mutum ne na gaskiya a Nijeriya, mai son jama’a da ci gaban kasarmu.
Ina kira gareku da ku zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Ya kasance abin dogaro kuma na yi imani zai gina kan nasarorin da muka samu.
A karshe ina kara tabbatar muku da cewa ina da cikakkiyar masaniyar irin wahalhalun da kuke fuskanta a halin yanzu sakamakon wasu manufofin gwamnati da ke da nufin kawo ci gaba a kasa baki daya.
Ina rokon ku da ku kara hakuri yayin da muke daukar matakan da suka dace don rage wahalhalu. In sha Allahu za a samu haske a karshen ramin.
Views: 11
