Labarin Yadda wata Mata da bata Jin zafi koda an yanki Fatar jikin ta

Labarin Yadda wata Mata da bata Jin zafi koda an yanki Fatar jikin ta

Kwararru sun ce sun gano yadda rikidewar kwayoyin halitta da ba kasafai ake gani ba ya bai wa wata mata damar yin rayuwarta ba tare da jin zafi ba ko an yanki fatar jikinta.

Masu bincike sun kwashe shekara 10 kafin gano yadda kwayoyin halitta ke sauyawa. A shekara ta 2013, wani aiki da aka yi a hannun matar mai shekaru 65 da haihuwa, Jo Cameron, ya sa an gano cewa kwayoyin hallitar ta sun rikide inda hakan ke hana ta jin zafin rauni.

Ta shaida wa BBC cewa, “An yi min tiyatar maganin amosanin gabbai a hannuna, da nake hira da mai aikin jinya, sai ya ce wannan aikin mai zafi ne sosai kuma bayan an gama za ka ci gaba da kasancewa cikin ciwo mai tsanani.”

“Sai na ce, ba za ayi haka ba, ba na jin zafin rauni,” bayan an gama tiyatar ya zo ya same ni ya tambaya, “ko kin sha wani magani ne. wannan abin mamaki ne.”

A lokacin da likitan Dr Devjit Srivastava ya ga cewa da gaske ba ta jin komai, sai ya aika ta zuwa wurin likitoci a jami’ar Landan da kuma Jamia’r Oxford.

Tawagar likitocin suka dauki jininta domin su gudanar da bincike kan kwayoyin halittar da ke jikinta.

Bayan sun kwashe shekaru shida suna bincike sai suka gano cewa sauyawar kwayoyin hallita mai suna FAAH-OUT da ke jikin Ms Cameron, shi ke hana ta jin zafin rauni da tsoro.

Views: 57

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *