Ɗaya daga cikin Alhazan Najeriya ya rasu lokacin da yake Sallah a Masallacin MANZON ALLAH SAW

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun

Ya Mutu Yana Sallah a Masallacin Manzon Allah SAW

Wannan Alhajin ya rasu bayan sallar Juma’a yana cikin yin sallar jana’izar wani a Masallacin Manzon Allah SAW ya yanke jiki ya faɗi nan take rai yayi halinsa.

Lallai wannan yayi ƙarshe mai kyau. Ya rasu a Masallacin Manzon Allah SAW. Ranar Jumma’a, da Alwala, Bayan Ya Idar da Sallar Farilla, Yana Sallahr Gawa, Ya taho daga Najeriya domin yin aikin Hajji.

Sheikh Huzaifi ne yayi mishi sallah kuma Sheikh Budair yana daga cikin maluman da suka raka shi maƙabarta aka binne shi a makabartar Baƙi’a da aka binne manyan Sahabbai.

Muna roƙon Allah ya jikansa da mu baki ɗaya.

Daga Auwal Saleh

Views: 10

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *