Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIL RAJU’UN
“Bata Gari Ke Neman Mu Da Sunan Su Yi Lalata Su Ba Mu Abcinci”
Inji-‘_ Wasu Yan Mata A Funtua
Wallahi wani abun akwai ban tausai bayan na daukesu munje gidannasu Chan karshen Unguwar Jabiri Cikin Garin Funtua Dake Jihar Katsina, naga halinda suke ciki sannan ga iyayensu kwance, mahaifinsu watanshi 6 a kwance, sannan mahaifiyarsu itama tana kwance dika babu lafiya, gashi babu namiji ko guda agidan dikansu mata ne su taimakonsu gashi kwana biyar batare dasunci abinciba.
Gidanda da suke Babu ‘kofa, Dakinda suke Babu ‘kofa babu taga, sannan Saman dakin daga gefe kana ganin waje idan damuna tayi dole sai dai sutafi zauren makwabta sukwana idan ana ruwa, Sannan wani lokacin haka yan iska suka shigo masu da daddare kokuma samari su rinka nunamasu suzo suyi iskanci dasu su basu abinci.
Mahaifin su bawan Allah ko lokacinda Yana da lafiya GADI yakeyi akasuwa, abunda yake samu kokudin cefane basa isarsa yanzu ga çiwo suma ‘yan uwanshi duk talakawanne Babu masu halin taimakonsu.
Bugu da ƙari sun dade suna Neman taimako Amma Allah besa sunsamuba, da sunan zuwa makaranta islamiyya da boko Amma saboda kuncin rayuwa dole suka dena zuwa, Ahaka suke zuwa gidajen maƙwabta idan akwai aiki wanki ko wanke wanke suyi abasu abinci su taho gida domin suci .
Jama’a Dangirman Allah ataimaki rayuwar wadannan ‘yanmatan akai mahaifinsu asibiti katsina , sannan ataimakesu da abinci dakuma kofofin gidan domin samun natsuwa, Idan Allah yabada dama hankalinsu yakwanta mumaidasu makarantar islamiyya dakuma boko din .
Domin Karin bayani Akira
👇
07060937266 Sadiq Umar yari.
Kokuma masu taimakawa ta banki ga account dinmu
👇
Acct. 1012016500
Keystone bank
SUY CHARITY FOUNDATION.
Kokuma account din ‘Yar uwarsu
👇
Acct. 1458351805
Access bank
Nana ABUBAKAR
Allah yabada ikon taimakonsu amin
Views: 31
