Malaman addinin Islama sun yi fashin baƙi game da kalmar “Inda Rabbana Ba Wahala”

Inda Rabbana Ba Wahala, wata kalma ce da ta samo asali a cikin wani shirin film ɗin Hausa mai suna A Duniya, wanda jama’a suka dunga yiwa fassara kala kala.

Abin har ta kai ga ana yiwa malaman addini tambayoyi game da wannan kalma ta Inda Rabbana Ba Wahala, a makon daya gabata.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa kalmar bada da wata illa kuma tana a kan dai dai da Tauhidi.

Yayin da Malam Abdullah Gadon Ƙaya shima ya ce lallai har Hadisai da ayoyin Alkur’ani mai tsarki, za’a iya kafa hujja da su kan cewa kalmar bata da wata matsala, sai dai bai kamata a riƙa furta taba a duk lokacin da za’ayi saɓon Allah.

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *