Malamin makarantar Allo ya yi garkuwa da ɗan ƙanin babansa a jihar Katsina

Jaridar Katsina Post ta ruwaito cewar, Malamin Makarantar Allo Ya Yi Garkuwa Da Dan Kanin Babansa A Katsina

Rundunar yan sandan jihar Katsina karƙashin jagorancin kwamishinan yan sanda, Alhaji Sanusi Buba ta yi nasarar cafke Malam Jamilu Idris, mazaunin garin Ƴankara, Sabon Fegi dake Karamar Hukumar Faskari a jihar Katsina bisa zargin sace yaro dan shekaru huɗu da haihuwa wanda dan kanin mahaifinsa dake garin Funtua ta jIhar Katsina.

Alaramma Jamilu Idris dan shekara talatin da tara da haihuwa ya je gidan kanin mahaifinsa, inda ya yi sallama yaron da ake kira Umar Faruq Kabir ya fito da yake ya san shi, kawai sai ya yi awon gaba da shi ya tafi da shi Abuja a wani gari da ake kira Dutsen Alhaji, inda ya damka shi hannun wata yar uwarsa ya ce mata almajiri ne kuma maraya ne.

Jamilu ya dawo Katsina, inda ya kira wo Baban yaro, ya ce sai an biya kuɗin fansa naira Miliyan biyar ko mu kashe shi, ya nemi sasancin zai ba da naira dubu dari biyar, Jamilu ya ki yarda, ya ga ba yadda zai ya rugo ya kawo wa rundunar yan sandan jihar Katsina rahoto, aka fara bincike muka kamo shi.

Alaramma Jamilu Idris ya amsa laifinsa a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai.

Views: 10

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *