Wani Miji ya saki Matarsa mai haihuwa bayan da yazo Asibiti yaga likita Namiji ne ya karɓi haihuwar ta
A jihar Katsina, rahotanni sun bayyana cewa wani magidanci ya saki matarsa ‘yar shekara 14 saboda wani likita namiji ya karɓi haihuwar ta.
A cewar jaridar Vanguard, matashiyar mahaifiyar ta samu matsala a lokacin nakuda wanda hakan yasa aka garzaya da ita asibiti.Sai dai cikin rashin Sa’a, babu likitoci mata a lokacin don haka sai Likita namiji ya shiga don Karɓar haihuwa.
Lokacin da mijin ya isa asibitin ya gana cewa wani likita namiji ya karɓi haihuwar matarsa, nan take ya sake ta.Dokta Fatima Adamu, babbar daraktar kungiyar Nana Women and Girls Empowerment Initiative, ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi a taron tattaunawa kan samar da lafiya na Human Resources for Health Production a Abuja.
Adamu ta roki gwamnatoci musamman a matakin jiha da su tabbatar an samu wakilcin ma’aikatan lafiya maza da mata a yankunan karkara.
Views: 19
