Mummunar Gobara ta ƙone wani sashe na layin dogo na blue a Legas

Yadda Mummunar Gobara ta kone wani sashe na layin dogo na blue a Legas.

Gobara ta kama wani sashe na sabon aikin sufurin jirgin kasa na Blue Rail Mass Transit a Marina jihar Legas.

Lamarin da ya faru a ranar Talata, 28 ga watan Fabrairu, 2023, ya sa mutane suka yi ta dirar mikiya, lamarin da ya haifar da turmutsitsi.

An tattaro cewa mutane da yawa sun yi kuskuren fahimtar faruwar gobarar a matsayin fashewa kuma sun yi tururuwa domin tsira.

Sai dai rahotanni sun ce gobarar ta shafa ne kawai bangaren da ke dauke da janareta da ake amfani da shi a ginin.

Haka kuma, ba a samu asarar rai ba, babu kuma wanda ya samu rauni, domin jami’an kashe gobara daga hukumomin kashe gobara na tarayya da na Jihohi sun yi gaggawar kashe wutar kafin ta bazu zuwa wasu sassa.

source alfijir hausa

Views: 35

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *