Zaben 2023: Bola Tinubu Ya Lashe Kujerar Shugaban Kasa

Zaben 2023: Bola Tinubu Ya Lashe Kujerar Shugaban Kasa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin zababben shugaban kasa.

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar ne ya bayyana nasarar Tinubu da misalin karfe 4:10 na safiyar Laraba.

Ya ce Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726 inda ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya samu kuri’u 6,984,520, yayin da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu 6,101,533, sai kuma Rabi’u Kwankwaso na NNPP wanda ya samu (1,496,687).

Ya ce sahihin kuri’u 24,025940 da kuri’u 939,278 da aka ki amincewa, yayin da jimillar kuri’un suka tashi a 24,966218.

Sanarwar wacce aka fitar a cibiyar tattara bayanai ta kasa da ke Abuja, ta yi nuni da kawo karshen kirgen da aka fara a ranar Lahadi.

Da yake bayyana sakamakon karshe, Shugaban INEC ya ce Tinubu da jam’iyyar APC suma sun cika sharuddan tsarin mulki.

Yakubu ya ce za a ba Tinubu da abokin takararsa Sanata Kashim Shettima takardar shaidar cin zabe da karfe 3 na yamma ranar Laraba.

Source: dimokuraɗiyya

Views: 26

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *