Mutane na amfani da lambar mu domin ciyo bashi — Rundunar ƴan Sanda tayi gargaɗi

Mutane na amfani da lambar mu domin ciyo bashi — Rundunar ƴan Sanda tayi gargaɗi

Jami’an ‘yan sanda a birnin Tarayya Abuja sun koka kan yadda ake amfani da lambobin gaggawa na hukumar don cin bashi.

Rundunar ta ce mutane na amfani da lambobin wurin cin bashin kamfanonin waya daban-daban da sauran laifukaKwamishinan ‘yan sandan birnin, Garba Haruna ya gargadi jama’a akan irin haka inda ya ce za su kama tare da hukunta masu aikata hakanFCT, Abuja – Rundunar ‘yan sandan babban birnin Tarayya Abuja ta gargadi ‘yan Najeriya kan amfani da lambobinsu na gaggawa don cin bashi.Kwamishinan ‘yan sandan birnin Tarayya, Haruna Garba shi ya bayyana haka a ranar Juma’a 28 ga watan Yuli a Abuja.

‘Yan sanda a birnin Abuja sun gargadi jama’a kan amfani da lambar su wurin cin bashi.Rundunar ‘Yan Sanda Ta Koka Yadda Mutane Ke Amfani Da Lambar Su Don Ciyo Bashi A Abuja.

Kakakin rundunar a birnin, Josephine Adeh a cikin wata sanarwa ta ce kwamishinan ya ba da umarnin kamawa da hukunta masu aikata hakan, TheCable ta tattaro.Ya gargadi jama’a ka amfani da lambar wurin cin bashi.

Ya roki jama’a da cewa irin wadannan lambobin gaggawa ba su dace da abin da ake aikatawa da su ba, amfaninsu shi ne kira don taimakon gaggawa.

Views: 23

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *