Na riga na buga Stamp ko second ɗaya ba zan ƙara a wa’adin daina karɓar tsoffin kuɗi ba—Emefiele

Babban bankin Najeriya CBN ya ƙara shelantawa ƴan ƙasar cewa yana nan akan bakan shi na daina amfani da tsoffin kuɗi daga ranar 31 ga wannan watan.

Bugu da ƙari gwamnan babban bankin ya ce ko second ba za’a ƙara a kan lokacin da aka ƙayyade ba.

A wani labarin kuma

Yayin da babban zaben 2023 ke gabatowa, wata tsohuwar jigo a jam’iyyar (APC) Hajiya Naja’atu Muhammad ta ce ba za ta sake maimaita kuskuren da ta yi akan Buhari ta yi kan Tinubu ba, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ba.

Najaatu ta ce ta bi Buhari ido rufe ba tare da wata ajanda ba kuma bai kamata a sake maimaita kuskuren ba.

A wata hira da tayi da gidan Talabijin na Trust a shirin Daily Politics, Najaatu ta ce ta bi Buhari tun 2022 kuma a karshe ya ci amanar yaddar da ta yi masa.

Ta ce, “Na bi Buhari kuma miliyoyin mutane sun bi Buhari saboda suna ganin zai gyara Najeriya amma ba mu taba ba shi ajanda ba, ba mu taba ba shi bukata ba, ba mu taba kulla yarjejeniya da shi kan abin da muke so ba. Don haka a wannan karon dole ne mu yi koyi da gogewa.

“Buhari ya watsar da dukkan mabiyansa, ya watsar da kowannenmu. Babu ɗayanmu da aka kai Villa. Kuma duk alkawuran da ya yi na cin hanci da rashawa, tsaro, noma da kuma bai wa ‘yan Najeriya muhalli, bai cika ba.

Najaatu ta ci gaba da cewa, “Yana aiki ne a kan gwamnatin da ta fi kowace gwamnati cin hanci da rashawa a Najeriya, ya yafe wa wasu manyan barayi a Najeriya. Za ku ji labarin wasu biliyoyin da aka sace kuma labarin an jefa shi ƙarƙashin kafet.

“A yanzu haka muna jin tiriliyoyin, to me yake cewa, yana ba da umarni kuma ana ba da umarni, ya bamu kunya, ya kasa cika alkawuran da ya dauka. Bayan na fadi haka, idan har zan iya yin kuskure a kan Buhari ba zan iya sake yin kuskure a kan Asiwaju ba.”

Ta kuma ce Tinubu ya shaida mata cewa ba shi da wani tsari ga arewa amma zai yi tsarin idan ya yi nasara. Ƙari ga haka, ta ƙara da cewa ba ta san tsananin rashin lafiyar Tinubu ba har sai da ta sadu da shi a Landan.

Views: 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *