Ni yar’uwar Buhari ce ta jini amma ya manta dani talauci zai kashe ni

Wata dattijuwa ta bayyanawa duniya cewa, ita yar’uwace ga shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari amma shugaban ya manta da ita a halin yanzu bara take yi domin samun abin kaiwa bakin salati kamar yadda ta bayyana a cikin wani fai fan bidiyo inda ta ce.

“Ni yar’uwa ce ta jini ga shugaba Muhammadu Buhari, kafin mahaifiyarsa ta rasu mun taba zuwa fadar shugaban kasa nida mahaifiyarsa lokacin yana mulkin soja, har mahaifiyarsa ta roki sojoji cewa don Allah koda kunyi masa irin wannan abin naku na sojoji, kar ku kashe min shi ku barshi da ransa, sai suka kwanta a gabanta suka ce baba babu abinda za muyi masa.

Ashe a lokacin ma har sun riga sunji juyin mulki, to bayan mun dawo daura daga nan ban kara ganin Buhari ba kuma ya’ya maza muke dani da shi, a yanzu ha bara nake kafin in samu abinda zan ci, in ji ta.

Views: 35

2 thoughts on “Ni yar’uwar Buhari ce ta jini amma ya manta dani talauci zai kashe ni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *