
Hausawa sunce so gamon jini wata kyakkyawar budurwa ta bayya soyayyarta a zahiri ga mai girma gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje.
Wannan zankadediyar budurwa kyakkyawa ta Shiga Shaukin soyayya da Gwamna Ganduje.
Budurwar mai suna Nana Adam Janbulo, tace tana matukar kaunar Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, kuma a shirye take ta aure shi, domin ta dauki tsawon lokaci tana son sa bada wasa ba, kuma tana neman wanda zai kaita wajen Ganduje domin ta Aure shi.
Yanzu haka Gwamna Ganduje dai a kalla yana da shekaru 73 a duniya, tare da matarsa guda daya tilo, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, tare da ‘ya’yansu guda bakwai.
Ku menene ra’ayoyinku shin ya kuke kallon Wannan Al’amari na Wannan Baiwar Allah?
Views: 160
