Sanatoci 50 daga cikin 109 sun sa hannu kan takardar tsige Gwamnan CBN—Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmed Lawan zai jagoranci sanatoci 50 domin su tsige gwamnan babban bankin Najeriya CBN.

Motocin dakon kuɗi da aka hango a gidan Tinubu a 2019 ɓatan-kai su ka yi, in ji ƙusa a APC

Wani ƙusa a jam’iyyar APC a jihar Legas, Ayodele Adewale, ya yi ikirarin cewa motocin dakon kuɗi guda biyu da aka gani sun nufi gidan dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, a jajiberin zaben shugaban kasa na 2019 “ɓatan-kai su ka yi.

Da yake zantawa da Arise TV a yau Alhamis, Adewale, wanda shi ne sakataren jam’iyyar na jihar, ya ce babu wanda ya gayyato motocin dakon kuɗin zuwa gidan Tinubu.

Ya ce: “A kan tambaya ta biyu na ko akwai wasu motocin dakon kuɗi ko babu, ina ganin wannan magana ta wuce.

“Babu kudi a cikin motocin. Duk yadda aka yi ɓatan-kai su ka yi su ka zo gidan na Tinubu .”

A tuna cewa tsohon gwamnan na Legas ya amince cewa motocin dauke da kudi ba takardun dangwala ƙuri’ar zabe ba ne ba kamar yadda masu sukarsa su ka yi ikirari.

Da ya ke jawabi ga manema labarai bayan kada kuri’arsa, Mista Tinubu ya ce yana da ‘yancin kawo kudi gidansa, yana mai jaddada cewa ba kudin gwamnati ba ne.

Views: 17

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *