
Mai alfarma sarkin musulmin Najeriya Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya shawarci masu riƙe da madafun ikon ƙasar nan da su ajiye su huta matuƙar ba za su iya sauke nauyin da Allah ya ɗora musu ba.
A lokacin da yake tsokaci kan matsalar tsaro a Najeriya a taron majalisar hadin kan addinai ta NIREC, Sultan Sa’ad Abubakar ya ce ba lokaci ba ne da mabiya addinai musamman Musulmi da Kirista za su rika zargin juna da yi wa juna barazana ba.
Sarkin Musulmin ya nuna damuwa kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jam’a ke ci gaba da afkuwa, amma kuma Musulmi da Kirista sun bige da nuna wa juna yatsa da yi wa juna barazana.
Views: 26
