Zan Raba Kogin Bahar Maliya Biyu Kamar Yadda Annabi Musa Ya Yi – Shaihin Tijjaniya
Duniya Mai Abubuwan Ban Mamaki; Wani Shehin darikar Tijjaniya Mutumin ƙasar Senegal yayi Alkawarin zai raba kogin Bahar Maliya zuwa Gida Biyu.
Wannan Mutumin da kuke gani Ɗan Asalin ƙasa Senegal ne, kuma babban jigo a darikar Tijjaniya ya kuma yi Alkawarin cewa Gobe Idan Allah ya kaimu zai raba kogin Bahar Maliya zuwa Gida Biyu kamar yadda Annabi Musa Alaihissalam yayi a zamanin shi.
Wannan Mutum ya gayyaci Ƴan Jaridu da dama domin su halarci wannan abun mamaki Wanda hankali ma baya ɗauka, a cewar shi Idan yayi Nasarar raba kogin zuwa Gida Biyu mai makon Ƴan ƙasashen Afrika su riƙa bin Jiragen Ruwa ko ta barauniyar hanya zuwa ƙasashen Turai yanzu zasu riƙa zuwa da ƙafaduwan su.
Kafar African profile tayi Alkawarin kasancewa a wurin domin ganin yadda zata kaya.
Shin yaya kuke kallon wannan bawan Allah kuma minene tunanin ku akan shi?
Views: 12
