Shugaban jam’iyyar APC Maimala boni zai gana da Jonathan da Kwankwaso

Wasu rahotanni na nuna cewa shugaban riƙo na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Boni zai jagoranci wata tattaunawa tsakaninsa da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da kuma tsohon gwamnan jihar Kano Eng, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ana sa ran tattaunar za ta share fagen dawo da Jonathan da Kwankwaso a cikin jam’iyyar ta APC, domin basu takarar shugabancin ƙasar a kakar zaben 2023.

Ana sa ran Jonathan zai yi takarar shugabancin kasar yayin da da Kwankwaso zai yi masa mataimaki.

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya da na fama da rikicin cikin gida wanda yaƙi ci yaƙi cinyewa.

Inda har wasu daga cikin masu adawa da jam’iyyar suka soma yin rubuta ce rubuce a kan wannan rikici.

Zazzafan rikici da rabuwar kai ya barke a cikin jam’iyyar PDP a dalilin fitar da dan takaran shugaban kasa.

Shugabannin jam’iyyar da suka fito daga kudancin Nigeria sunce dole ne wanda zai tsaya takaran shugaban kasa a PDP ya fito daga kudancin Nigeria kuma wanda ba Musulmi ba.

Sai dai wannan batu ya tashi hankalin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka fito daga yankin Arewa, sunce sam ba zasu yadda ba, a halin yanzu suna cacar baki wanda alama ke nuni da rugujewar jam’iyyar.

Kwanakin baya VOA tayi hira da Buba Galadima yace har yanzu dai halin rashin gaskiya da aka san PDP da shi yana nan babu abinda ya canza, wanda hakan ke nuni da cewa shima ya fice daga jam’iyyar.

Views: 4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *