Shugaban Twitter ya wallafa tutar Najeriya har sau uku a shafinsa

Yau kimanin makonni biyu kenan tun bayan da gwamnatin tarayyar Najeriya ta rufe shafin sada zumunta na Twitter, ake ta samun maban bantan ra’ayoyin game da matakin.

A wani saƙo mai cike da rudani, shugaban Twitter Jack Dorsey ya wallafa tutar Najeriya sau uku ba tare da wani bayani ba.

Sai dai wasu daga cikin jaridun Najeriya sun fassara saƙon a matsayin nuna goyon baya ga zanga-zangar da aka yi ranar Asabar da ƙasar ke bikin dimokuraɗiyya a kasar.

Hakazalika saƙon na shugaban Twitter ya ja hankalin ƴan Najeriya musamman waɗanda ke ci gaba da amfani da shafin ta wata hanya ta daban duk da haramta amfani da Twitter da gwamnatin Najeriya ta yi a ranar hudu ga watan da muke ciki.

Sai dai har yanzu kamfanin na Twitter na cigaba da tattaunawa da gwamnatin Najeriya kan haramta ayyukansa da gwamnatin ƙasar tayi.

Views: 15

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *