
Za a daura auren Tagwayen Asali (Hassan Sani Abubakar da Hussaini Sani Abubakar)
Kamar yadda kuka sani ƴan biyu su auri ƴan uwansu tagwaye ba sabon abune ba musamman a tarayyar Nijeriya.
Domin kuwa ko a shekarar da ta gabata an samu waɗanda suka auri ƴan uwansu tagwaye a ƙaramar hukumar Malumfashi dake a jihar Katsina.
Sai gashi a yanzu haka ma tagwaye za su auri tagwaye a Katsina
Za a daura auren Tagwayen Asali (Hassan Sani Abubakar da Hussaini Sani Abubakar) da Hassana Abdu Bawa da kuma Hussaina Abdu Bawa a Dutsin-Ma jihar Katsina ranar Asabar 8 ga watan Janairun 2022.
Allah Ya sanya alheri
Views: 12
