Tinubu ya bayyana abinda suka tattauna da sarakunan gargajiya kuma ya nemi alfarma 1 a wajen su
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sarakunan gargajiya su goyi bayan manufofin gwamnatinsa
Ya yi wannan kiran ne ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, a yayin wata ganawa da ya yi da sarakunan gargajiya a fadarsa da ke Abuja
Shugaba Tinubu ya kuma ba su tabbacin cewa za su samu goyon bayan gwamnatinsa domin su yi ayyukansu yadda ya kamata
FCT, Aso Villa – Sakamakon ganawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi da sarakunan gargajiyan Najeriya ya bayyana.
Shugaba Tinubu, ta wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, ya bayyana cewa ganawarsa da sarakunan ta yi kyau, inda ya bayyana cewa ya samu kyakkyawar alaƙa da su a yayin ganawar.
Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya
Tinubu ya nemi sarakunan gargajiya su bai wa gwamnatinsa hadin kai. Hoto: @OfficialABAT Asali: Twitter

Tinubu ya nemi sarakunan su marawa gwamnatinsa baya
Tinubu ya buƙaci masu rike da sarautun na gargajiya, da su haɗa ƙarfi da ƙarfe su mara wa gwamnatinsa da manufofinsa ga ‘yan ƙasa baya.
A cewar Tinubu a shafinsa na Tuwita:
“Na ji daɗin zama na, a safiyar yau, da taron sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban na ƙasar nan.”
“A yayin tattaunawar mu, na ba su aikin tallafawa ƙoƙarin da gwamnati ke yi na samun dawwamammen zaman lafiya da haɗin kai ta hanyar ɗabbaƙa halayen kirki da kishin ƙasa.”
Tinubu ya ɗaukarwa sarakunan alƙawari
Shugaba Tinubu ya kuma ba su tabbacin cewa, zai ba su dukkanin goyon bayan da suke buƙata don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, a matsayinsu na jakadun al’adun Najeriya.
Taron dai na daga cikin jerin abubuwan da shugaban ya yi da masu ruwa da tsaki tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’adu Abubakar, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero Obi na Onitsha, Alfred Achebe, Oba Elegushi, Alayeluwa Saheed Ademola da ƙarin wasu da dama
Source:Hausa.legit.ng
Views: 19
