Tirƙashi: “Ba zan iya Auren mai albashin ₦70,000 ba— inji wata budurwa

Ba zan iya Auren mai albashin ₦70,000 ba— inji wata budurwaWata budurwa ‘yar Najeriya ta ce ba za ta iya auren mutumin da albashinsa N70,000 bane, ta jawo.

cecekuce.Budurwar ta nuna alamar turbune fuska tare da cewa ai kudin sun yi kadan wajen kula da ita, ta bayyana dalilinta.‘Yan Najeryan da suka yi martani a bidiyon sun ce ta yi ganganci, domin ba kowa ne cikin ma’aurata ke samun N70k ba.Wata kyakkyawar budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana irin ‘yan albashin da ba za ta iya aura ba a wani bidiyon da @kikiotolu ya yada.Budurwar ta ce, ba za ta iya auren mutumin da ke samun N70,000 ba a wata.

Ta kara da cewa, kudin sun yi kadan wajen kula da alakarsu.Ga batun aure kuwa, ta ce kudin sun yi kadan, domin ta san aukin kudin saboda ita ma N70,000 take samu duk wata.Ba zan auri mai albashin N70k ba, inji wata budurwaBudurwar da tace ba za ta aurei mai albashin N70k ba. Hoto: @kikiotolu Asali: TikTokAmsan da ta bayar bayan tambayarta ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta.

mutane da yawa sun yi martani mai daukar hankali.Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, bidiyon ya samu martani sama da 2000 da kuma dangwalen nuna sha’awa sama da 18,000.

source: hausa.legid.ng

Views: 34

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *