CIGIYA: Wata Bazawara Ma’abociyar Zikiri Da Wazifa, Tana Neman Mijin Aure Mabiyin Darikar Tijjaniyya A Kano
Wata bazawara da take da yara biyu tana neman mijin aure a Kano. Ta ce tana son namiji mai tsoron Allah mai neman na kansa, mai ilimin qur’ani kuma Dan Tijjaniya saboda ma’abociyar zikiri ne da wazifa.
Saidai Allah ya jarabce ta da cuta mai kashe garkuwar jiki, wato sida.
Ita dai wannan baiwar Allah a yayin da RARIYA ta ji ta bakin ta kan yadda aka yi ta kamu da cutar ta kanjamau, ta bayyana cewa “Wato tun ina karama ‘yar shekara 13 aka yi mini aure. Da yake kakata ta hada auren da dan kawarta domin zumuncinsu ya kara kulluwa. Amma ba ta san cewa ba shi da lafiya ba. Sai lokacin da na zo haihuwa na biyu shine aka sanar da ni”.
Matar mai kimanin shekaru 30, ta kara da cewa ” hankalin ta ya yi matukar tashi bayan da aka sanar da ni cewa ina dauke da cutar ta sida, wanda a dalilin haka ya sa na fada a gida shine iyayena suka ce sai an yi bincike a ga ni da shi wa yasawa wani. Inda bayan an bincika sai aka gano ashe ya dade yana shan magani saboda yana dauke da cutar.
“Daga karshe dole haka da muka rabu ba don muna so ba. Kuma baban mu ya so ya kai maganar kotu sai aka hana shi aka ce saboda kada ya bata min suna. Kawai a bar shi da Allah, kuma kakata ta yi ta kuka, tana ce ta san ita ta ja min. Ni kuma na ce ta daina damuwa haka Allah ya kaddara”.
Yanzu dai duk wanda ya gamsu da bayanan ta kuma ya amince har ga Allah zai aure ta, zai iya tuntubar RARIYA domin a ba shi lambarta su tattauna domin su daidaita.
Views: 179
