Jami’an Hisbah na jihar Kebbi sun kama wasu matasa 9 da laifin aikata lalata
Matasan da suka hada da maza da mata biyar, an kama su ne a wani masaukin baki da ke Birnin Kebbi a daren Litinin, 24 ga Afrilu, 2023.
An kama wasu matasa tara bisa zarginsu da hannu wajen aikata lalata.
Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kebbi ne suka damke matasan.
Matasan da suka hada da maza da mata biyar, an kama su ne a wani masaukin baki da ke Birnin Kebbi a daren Litinin, 24 ga Afrilu, 2023.
Kwamandan Hisbah na jihar Kebbi, Ustaz Sulaiman Muhammad, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce jami’ansu sun kai farmaki kan bakon.
Views: 95