Tofa Rarara ya yiwa Ganduje wankin babban bargo a sabuwar waƙar Mai Dala da ya saki

Shaharren mawaƙin siyasar Najeriya Dauda Abdullahi Adamu Kahutu Rarara ya saki kaɗan daga cikin sabuwar waƙar da ya rerawa mai taken mai dala wacce ake zargin yana yin shaguɓe ne ga mai girma Gwamnan jihar Kano.

A ƙarshen makon daya gabata ne ɗan takarar neman kujerar shugaban Najeriya Alhaji Ahmed Bola Tunubu ya gudanar da yaƙin neman zaɓen sa a jihar Kano inda aka ƙi gayyato Rarara domin gudanar da waƙoƙin sa a wajen taron.

A wani labarin kuma.

Yadda ake

Ziyara Zuwa Wajen Ibada Mafi Wahala A Duniya.

Abune Yemanta Guh, Coci ne guda ɗaya wadda yake a gundumar Hawzen na yankin Tigray a Habasha. Ya na da tsayin mita 2,580 (ƙafa 8,460) kuma dole ne a hau da ƙafa don isa. Sanannen waje ne saboda zane-zane a jikin bango wadda aka zana a ƙarni na Biyar da kuma gine-ginensa.

A cewar Almara a ƙasar Habasha, an sassaƙa Cocin a ƙarni na Biyar kuma an sadaukar da shi ga Abuna Yemata (wanda ake kira Abba Yem’ata), ɗaya daga cikin Waliyyai Tara.

An yi imani da cewa, tsarkaka Tara sun samo asali ne daga Roma Konstantinoful da Siriya tsakanin ƙarshen ƙarni na Biyar da farkon ƙarni na Shida.

Habasha ta kasance ɗaya daga cikin rukunan addinin Kirista na farko a duniya, kuma Cocin Orthodox, wadda Abuna Yemata Guh ke cikinta, na ɗaya daga cikin tsofaffin ɗarikun addinin.

Duk da Yanayin da ake fama da shi a yankin amma ana kiyaye zane-zanen Cocin na ƙarni na Shida, wadda aka yi da kitsen dabbobi.

Abuna Yemata Guh, ana ɗaukarsa ɗaya daga cikin mafi kyawun Majami’u a Habasha. Don zuwa nan, dole ne ku ratsa tsaunukan dutsen yashi mai tsayi.

Uba Yemata ne ya sassaƙa Cocin da aka sassaƙa da dutse a ƙarni na Biyar. Ba a san dalilin da ya sa ya zaɓi irin wannan wuri mai nisa ba, duk da haka rahotannin tarihi tun daga lokacin sun ba da rahoton an tsananta wa Habashawa tsirarun Kiristoci a lokacin, don haka mutane da yawa su na kyautata zaton ya na gujewa maƙiya da kama shi.

Wasu kuma su na da’awar Yemata ya na neman kaɗaici da keɓewa daga duniya, ya na neman wurin da zai yi tunani a cikin bege na samun Allahntaka na gaskiya .

Views: 13

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *