Ɗan takarar neman kujerar shugaban Najeriya a ƙarƙashin jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ta bayyana muhimman ayyukan da zai fara gabatarwa da zarar an rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya idan ya lashe zaben shugaban kasa.
Atiku yace zai mayar da hankali wajen ganin cewa tsaro ya inganta a ƙasar nan sannan zai sauya fasalin yadda ƙasar ke tafiyar da tattalin arzikinta daga tsohon tsarin bankuna zuwa degital currencies system sannan zai tabbatar da cewa ya bunƙasa harakokin ilimin boko a ƙasar.
Atiku Abubakar ya ƙara da cewa zai inganta harakokin kiwon lafiya mata da yara ƙanana zasu samu kulawa a asibitocin gwamnati kyauta.
Sannan zai bincika yaga su wanene suka sace dukiyar ƙasar musamman tsofaffin Shugabannin ƙasar domin ya ƙwato ta a duk inda suka kaita tare da kama su.
Wannan bayani na Atiku Abubakar ya jawo hankalin masu sharhi game da harakokin da suka shafi siyasa inda wasu ke ganin tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo na kan gaba daga cikin waɗanda Atikun zai fara damƙa, ko da yake shi a nashi ɓangare Atikun bai ambaci sunansa ba.
Dama dai tsohon shugaban na Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ya sha nanata cewa ba zai taɓa goyawa Atiku Abubakar baya domin ya zama shugaban Najeriya ba inda har yake cewa Allah ma ba zai yafe masa ba idan yayi hakan.
A wani labarin kuma.
Kwankwasiyya Ta Tsoratar Da Zulumiyya A Jihar Borno
Wasu matsoratan ‘yan siyasa a jihar Borno sun tura ɓata gari inda su suka farfasa billboard mai ɗauke da hoton ɗantakaran Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da na ɗantakaran kujeran Sanatan Borno Central H.E Attom Magira
Majiyar ta ce, Manyan billboard ne da a kafesu a sassan gurare masu muhimmanci dake cikin birnin Maiduguri, amma yau an wayi gari duk an lalata su.
An tabbatar da cewa, jagoran jami’ar NNPP a jihar Borno H.E ATTOM MAGIRA ya nuna jarumta wajan tallata jam’iyyar NNPP a jihar Borno, da alama farin jinin Kwankwasiyya ya tsorata Zulumiyya a Borno tin da a kwanakin baya har ofishin NNPP aka rufe a birnin Maiduguri.
Masu sharhi a kan siyasa sun bayyana cewa, babu shakka irin wannan mataki da suke ɗauka na bangar siyasa babu abinda zai yiwa jam’iyyar NNPP a Borno sai ƙarin ƙarfin gwiwa, sannan talaka a Borno zai ƙara fahimtar waye APC kuma su waye jagororinta, kuma talaka zai gane waɗancan mutanen basu cancanta zu wakilceshi ba ko kuma su jagorance shi.
Views: 6
