Fitaccen ɗan kasuwar Afrika Abdussamad BUA ya ce fiye da shekaru da 30 da suka wuce Ɗangote yana mana bita da ƙulli don ganin bayan mu kuma zamu ƙara rage farashin kayanmu

A wata wasiƙa da Kamfanin BUA na Attajirin ɗan kasuwa Alhaji Abdussamad Isyaku Rabi’u, ya fitar da dogon jawabi a matsayin martani ga zargin da kamfanin Dangote Group ya jefe sa da shi.
A wasikar da ta fitar ga duniya, BUA Group ya karyata Dangote, kan wani batu.
An jima sosai tsakanin Abdussamad Isyaka Rabiu da Aliko Dangote ana gwabzawa.
Kamfanin na BUA ya dauko tarihi tun daga 1991 lokacin da aka yi wahalar sukari, amma sai aka yi sa’a Abdul Samad Rabiu yana da sukari a kasa.
BUA ya ce Aliko Dangote ya nemi a saida masa sukarin, sai a karshe lamarin ya kare a kotu, kamfanin ya ce haka Rabiu ya jajirce na watanni uku.
Har ila yau, kamfanin ya ce ya taba karban aron fili daga Usman Dantata domin ya kafa kamfanin siminti, amma Dangote ya jawo aka karbe filin.
A dalilin wannan abin da ya faru a gwamnatin Olusegun Olusegun Obasanjo, BUA ya yi asarar filin da ya karbi aro daga hannun kawun na Dangote.
Wasikar ta ce haka kamfanin ya yi ta fama bayan samun lasisin kafa kamfanin siminti, BUA ya ce sam kalubalen nan ba su iya taka masu burki ba.
A wani rahoto da Leadership ta ruwaito ya bayyana yadda aka dilmiyar da kimanin Dala Biliyan 3 da ta samo asali daga CBN a kamfanin Ɗangote tun a Gwamnatin baya.
Tunda fari an hango wani martani da Ɗangote ya yi ne, na zargin BUA da biyan yan jaridu kuɗi don wallafa labarin karya a kansa.
Hakazalika BUA na zargin Ɗangote da yunkurin bin duk wasu hanyoyi da zai durkusar da su tun a shekarun baya.
Meye Ra’ayin ku?
Views: 69
