Video: “ku kalli yadda magoya bayan ɗan majalissa suke keta haddin matashiya Fadila

Hon Engr Ahmad Satomi Ya Fitar Da Takardar Neman Ya Fiya Kan Cin Zarafin Da Yaransa Suka Yi Wa Fadila Abdurrahman.

Wannan itace takardar da ya fitar.

Daga Ibrahim Da’u Mutuwa Dole.

Dan majalisar Jere, Engr Ahmad Satomi ya fitar da takardar neman ya fiya akan wulakanci da wasu yaran sa Sukayi ma Fadila Abdurrahman, har wajen kasuwanci ta.

Fadila Abdurrahman tayi wani rubutu akan uban gidan nasu Engr Satomi, wasu daga cikin yaransa sunje sun ci mutunci Fadila Abdurrahman tare da farfasa mata shagon kasuwancin ta.

Sakamakon kiraye kiraye, da rashin nuna jin dadi da al’umma suka nuna, akan abin da waɗannan yaran na Satomi suka yi ma Fadila Abdurrahman, haka yasa shi Hon da kanshi ya fitar da takardar neman ya fiya.

Views: 21

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *