VIDEO: “Ku kalli yadda Zakir Naik ke cigaba da Musuluntar da kiristoci a Qatar”

Rahotanni daga ƙasar Qatar inda ake gudanar da gasar cin kofin Duniya na cewa shahararren malamin addinin Islama na duniya Sheikh Dr. Zakeer Naikh na can yana ci gaba da musuluntar da kiristoci.

Inda kawo yanzu jumillar waɗanda ya samu nasarar jawo su zuwa cikin addinin na Islama ya kai kimanin mutane dubu 5,000 da ɗoriya.

Dama dai tun farkon buɗe wannan gasa a ƙarshen watan Nuwamban da ya gabata ƙasar ta Qatar ta gayyaci shehin malamin domin gudanar da da’awa.

A wani rahoton kuma.

Rundunar Ƴansandan Jihar Benuwai Ta Gayyaci Mutumin Da Aka Samu Rubabbin Kuɗi A Shagon Shi

Daga Muhammad Aminu Kabir

Mai magana da yawun Rundunar Ƴansandan a Jihar Benuwai ya bayyana cewa bayan da suka samu Rahoton waɗannan kuɗaden sunyi bincike tare da gayyato mai wurin dake cikin Wadata Barracks domin amsa tambayoyi.

Mai wurin Sulaiman ya bayyana cewa yanada lasisi daga babban bankin Najeriya CBN akan ya sarrafa Rubabbin Kuɗi, a cewar shi suna amfani da Rubabbin kuɗin ne wajen yin maganin sauro.

Rundunar Ƴansandan tace zata faɗaɗa bincikenta har zuwa Babban Bankin Najeriya domin tabbatar da abinda Wanda ake tuhumar ya bayyana.

Views: 8

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *