Video: “Muhimmiyar sanarwa kan cigaban shirin Labarina daga Aminu Saira”

Labarina wani ƙasaitaccen shirin wasan kwai kwayo ne mai dogon zango wanda kamfanin Saira Movies ke shiryawa.

Kuma ake gabatar da shi a tashar talabijin ɗin Arewa24 a ko wace ranar juma’a.

To sai dai wasu daga cikin masu kallon shirin sun ga an daina kawo musu shi kamar yadda aka saba.

Wanda kuma hakan ya biyo bayan ƙarewar Season 3 na ahirin inda yanzu haka ake ci gaba da ɗaukar Season 4.

Ma shiryin shirin wato Malam Aminu Saira, ya wallafa wani faifan bidiyo a shafukansa na sada zumunta.

Inda ya bayyana cewa jama’a su yi haƙuri sakamakon rashin sanar da su da aka yi da wuri amma a halin yanzu.

Sun tafi hutu za su ci gaba da ɗauakar shirin kafin su dawo da haska shi.

Views: 51

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *