Kamar dai yadda kuka sani ƴan mata da samari na baje kolinsu a shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media.
Inda wasu ke amfani da kafafen na sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram, da dai sauransu wajen gudanar da harakokin da suka shafi kasuwanci.
Wasu kuma ke yin rubuce-rubuce da nufin jan hankalin mabiyansu wato followers, ta yadda za kuga ƴan mata da samari na yin abubuwan da zasu ɗauki hankulan abokansu na sada zumunta.
A nan wata budurwa ce ta bayyana cewa a halin yanzu duk duniya babu abinda take so kamar aure.

A wani labarin kuma
Gwamnan Zamfara Ya Dakatar Da Yakin Neman Zaben APC A Jiharsa
Daga Nura Ahmad Hassan
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta dakatar da shirin yakin neman zabenta har zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2023 saboda wasu dalilai da har yanzu ba a bayyana ba.
DAILY POST ta ruwaito cewa jam’iyyar a jihar ta ce jami’an yakin neman zaben ta sun yanke shawarar daukar hutu, inda suka ce jam’iyya mai mulki ta yi ta mai da hanakali wajan fafutukar ganin an dawo da zaman lafiya a jihar.
“Na riga na yi alkawari cewa a wa’adina na biyu, zan dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara”.
Gwamna Matawalle ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da yakin neman zabensa a karamar hukumar Kaura Namoda a jihar a makon jiya Talata 27 ga watan Disamba 2023.
Abaya Dimokiradiyya ta ruwaito cewa Gwamna Matawalle ya nada tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari a matsayin kodinetan yakin neman zabensa a jihar ta Zamfara
Sai dai tsohon Gwamnan ya yi kira ga mazauna jihar inda ya jaddada cewa za a magance matsalar rashin tsaro a jihar idan Matawalle ya dawo kan karagar mulki.
Majaiyar Dimokuradiyya na iya bayar da rahoton cewa Tsoffin Gwamnonin Jiha sun halarci shirye-shiryen yakin neman zaben, inda suka nuna cewa suna goyon bayan Matawalle gaba daya domin ya ci gaba da rike mukamin na sa.
Views: 9
