Kamar dai yadda kuka sani ƴan mata da samari na baje kolinsu a shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media.
Inda wasu ke amfani da kafafen na sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram, da dai sauransu wajen gudanar da harakokin da suka shafi kasuwanci.
Wasu kuma ke yin rubuce-rubuce da nufin jan hankalin mabiyansu wato followers, ta yadda za kuga ƴan mata da samari na yin abubuwan da zasu ɗauki hankulan abokansu na sada zumunta.
Wata matashiya mai suna Hauwa’u mai amfani laƙabin Jiddarh a shafin ta na Twitter ta bayyana cewar “Wallahi Miji Nagari wahala yake” ga hoton Screenshot ɗin rubutunta nan daga ƙasa.

A wani labarin kuma
Wata jami’a a Nijeriya ta hana ɗalibai amfani da wayoyin zamani
Jami’ar Bingham da ke Karu, a Jihar Nasarawa ta fitar da sanarwar hana dalibai amfani da wayoyin zamani
Sanarwar, mai ɗauke da kwanan wata, 18 ga Janairu ta sanar da ɗalibai cewa an ɗauki matakin ne biyo bayan karya dokokin makaranta game da amfani da wayar hannu na zamani.
Sanarwar ta kara da cewa, “Bayan karya dokoki akai-akai wajen amfani da wayoyin hannu, wanda ya saɓa wa sashe na 5.14 karamin sashe na I, II da III na littafin jagoranci ga dalibai, an haramta amfani da wayoyin komai-da+ruwanka da gaggawa.
“Za a kwace wayoyin waɗanda su ka karya wannan doka kuma za su fuskanci hukunci da ya dace.”
Sanarwar ta ƙara da cewa bayan hana amfani da wayar hannu ta zamani, jami’ar ta ce dalibai na iya amfani da kwamfutocin su.
“Eh, mun hana amfani da wayoyin zamani kamar yadda aka bayyana a cikin bayanin magatakarda amma muna ba da izinin amfani da kwamfyutoci,” in ji sanarwar.
Views: 5
