Jaridar Legit hausa ta bada rahoton cewa, wata mata a ƙasar Amurka ta bayyana yadda take bai wa mijin ta damar kwanciya da mahaifiyar ta da ‘yar’uwar ta.
Madi Brooks ‘yar Amurka ce ta bayyana wa mabiyan ta na TikTok wadanda sun wuce mutane 92,700 dangane da rayuwar auren ta.
Matar, mahaifiyar ta da mijin ta su na rayuwa yadda su ka ga dama, sannan har kanwar ta ma ba su bari a baya ba.
“Ni da mahaifiya ta mu na musayar miji na wurin kwanciya, kuma hakan ya na da kayatarwa kwarai.
“Kun san dalili? Idan na ji ba zan iya ba shi kai na ba, sai in ba shi damar kwantawa da ita. “Eh! Ni irin matar nan ne. Ba na bai wa miji na kaina sai sau 2 a mako.”
Views: 25
