Wata Amarya mai suna Khadija Abdullahi ta makance a ido ɗaya sakamakon zabga mata gora da ‘yan ƙato da gora suka yi
Wannan ibtilain dai ya faru da Khadijah ne ana tsaka da shaglin bikin ta a unguwar Ɗantamashe da ke Kano.
A cewar Khadija Ƴan kungiyar sintiri na Vigilante na unguwar su ka yi mata wannan aika-aikan lokacin da suka zo raraka ana tsaka da kidan DJ.
A wani labarin kuma
Ɗan Majalisar Tarayya a Zariya Ya Maka Ɗan Jarida Saifullahi Lawal imam Zariya a Kotu.
Zababben Dan majalisar Tarayya mai wakiltar Zariya Hon Dr Abbass Tajuddeen ya Maka fitaccen matashin dan jaridar nan dake Zariya Saifullahi Lawal Imam a kotu bisa zargin yana so ya bata masa Suna da zubar masa da mutunci.
Dan Majalisar dai ya kai Dan jaridar kotu ne a shekaran jiya Alhamis, za a shiga kotun ranar biyu ga watan fabairun mai zuwa.
A zantawa da aka yi da matashin dan Jaridar akan wannan lamarin, ya bayyana cewa shi bai ma san abunda ake zarginsa da shi ba, domin bai san mai yayi wa dan majalisar ba da har aka kai shi kotu.
. Saifullahi Lawal Imam ya kara da cewa “Ni tsohon yaron gidan Dan majalisar Tarayyar ne, tun shekara ta 2015 nake gidansa ina masa hidima,
ina kareshi daga abokan adawa da kare masa kima da mutunci, ban taba neman komai a wajensa ba, domin saboda Allah nake kaunarsa, Al’amarin ya farune lokacin da wata cuta ta kamani a kunnena wacce ke barazanar kurumtar dani,
inda na bukaci taimakon Dan majalisar wanda na dauka kamar uba a gareni akan taimakamun domin a mun aiki, inda yayi Alkawarin zai yi nemarmun taimako don ganin mun magani in cigaba da jin magana, amma tsawon lokaci watanni da dama bai taimakamun ba duk da Biyayyata da Sadaukarwata ga siyasar Gidansa, wanda Sau uku ana kulleni a Caji Offis saboda kare masa mutunci daga abokan adawa,
ganin ciwon na cigaba da tsanantawa har gashi na daina jin magana tasa na yanke shawarar barin tafiyar Gidansa Sabili da la’akari da na yi da cewa ba za a taba taimakamun a gidan siyasarsa ba duk da Sadaukarwata a gareshi”.
“Bayan na bar tafiyar gidan nasa na koma gidan babban abokin adawarsa na jam’iyyar Labour Party Wato Hon Suleiman Ibrahim Dabo wakili, A duk rubuce-rubucen da nake na tallata Wakiline amma sai gashi an kawomun Sammaci wai na batawa dan majalisar Tarayya Suna ba tare da na san ta yaya hakan ta faru ba”
Saifullahi Lawal Imam wanda kuma mambane a kungiyar Jaridun kafafen Sadarwa na zamani, kuma Mamba a kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty international da kuma Human Right Network ya danganta lamarin da bita da kulli don ganin bayansa, inda ya bayyana cewa hakan ba zai taba Samun nasara ba..
A na su martanin Kungiyar Yan Jarida ta kasa A wani zama da sukayi jiya a kaduna sun bayyana cewa suna jira ne su ga motsin da dan majalisar zai yi akan mamba na su wato Saifullahi Lawal Imam kafin daukar mataki.
Suma kungiyar Kafafen yada labarai a Dandalin Sadarwar Zamani
Views: 24
