Shafin Legit hausa ya ruwaito cewa, wani matashi ya auri dattijuwa ƴar shekaru 61 a duniya.
Matashin dan shekara 24 mai suna Quram ya auri masoyiyarsa Cheryl bayan shekaru takwas suna tare Sabuwar amaryar yar shekara 61 ce.
Kuma tana da ‘yaya takwas, amma duk da haka Quram yace yana matukar son ta Ya bayyana yadda suke soyewa kullu yaumin kuma tana matukar bashi sha’awa.
Soyayya akace makauniya ce kuma hakan ya bayyana karara a labarin soyayyar dan shekara 21 Quram da sabuwar Amaryarsa yar shekara 61 Cheryl.
Tun lokacin da labarin aurensu ya yadu a kafafen sada zumunta, mutane na tofa albarkatun bakinsu kuma masoyan sun bayyana yadda suke matukan son juna.
Views: 14
